IQNA

Koyar Da Dahuwar Abincin Halal A Afirka

23:45 - October 10, 2017
Lambar Labari: 3481987
Bangaren kasa da kasa, hukumar kula da harkokin yawon bude ido a birnin Cape Town a Afirka ta kudu na daukar nauyin koyar da dahuwar abincin halal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bizcommunity cewa, hukumar kula da harkokin yawon bude ido a birnin Cape Town a Afirka ta kudu na daukar nauyin koyar da dahuwar abincin halal karkashin kulawar shirin Crescent Rating wanda Muhammad Kamal Da Jawid Ahmad daga Singapore suke jagoranta.

Babbar manufar shirin dai ita ce mayar da abincin halal ya zama daya daga cikin muhimman nauoin abinci da ake samu a wuraren cin abinci an birnin.

Hukumar ta yi la'akari da cewa, rashin samun abincin halal a wuraren yawon bude yana kawo nakasu a wasu lokuta na rashin samun musulmi yadda ya kamata, domin musulmi da dama sukan yi amfani da abincin halal ne kawa.

Bisa la'akari da cewa akwai musulmi da suke zuwa wurin kuma suna fuskantar matsala ta abinci, wannan ya sanya hukumar ta dauki nauyin horar da wasu masu gidajen abinci yadda za su rika samar da shi.

3651413


captcha