IQNA

Kungiyar OIC Ta Yi Kirayi Da A Kawo Karshen Kisan Musulmi A Kasar Sri Lanka

22:23 - March 08, 2018
Lambar Labari: 3482463
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kira da a kawo karshen kisan musulmi a kasar Sri Lanka ba tare da wani bata lokaci ba.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya habarta cewa, a cikin bayanin da kungiyar ta OIC ta fita ta bayyana cewa, kisan musulmi a kasar Sri Lanka ba abu ne da za a amunce da shi ba, a kan dole ne  a kawo karshen hakan cikin gagagwa.

Bayanin ya kara da cewa wannan nauyi ne da ya rataya a gwamnatin kasar ta Sri Lanka, kuma babu wata hujja da zata sanya a yi ta yi wa muuslmi isan kiyashi babu gaira babu sabar a kasar.

A cikin makon nan ne aka kasha wani dan addinin buda a kasar Sri Lanka a wani rikici da ya hada shi da wasu mutane, amma sai ‘yan adinin buda suka danganta kisan nasa da musulmi, wada hakan ya sanya wasu masu tsatsauran ra’ayin adinin na buda suka kaddamar da farmaki kan gidajen musulmi da shagunansu da sauraren wurarensu.

3698069

 

 

 

 

 

 

captcha