IQNA

Cututtuka Masu Kisa Na Ta Kara Bazuwa A Cikin Kasar Yemen

21:45 - March 11, 2018
Lambar Labari: 3482468
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Yemen na nuni da cewa ana kara samun karuwar cututtuka masu kisa a kasar sakamakon matsalolin da ake fuskanta a bangaren kiwon lafiya.

Kamfanin dillancin labaran Alarabi jaded ya habarta cewa, sakamakon killace kasar Yemen da kuma kaddamar da yaki a kanta da sojojin Saudiyya ke ci gaba da yi tsawon shekaru uku a jere, cututtukla masu kisa musamman ga kanan yara suna ci gaba da kara bazuwa a wasu yankuna na kasar.

Abdulhakim Alkahlawi kakakin ma'aikatar kiwon lafiya a kasar Yemen ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu bayan cutar kwalera, cutar kyanda ce take addabar yara, kuma babu magunguna da za a ba sua  asibitocin kasar, domin Saudiyya ta hana a shigar da magunguna da abinci a kasar, wanda hakan yasa yara da dama suna ci gaba da mutuwa.

Ya kara da cewa ya zuwa garuruwan Baida, Miras, Walid rabi da Madina su ne lamarin yafi Kamari a cikinsu.

3698834

 

captcha