IQNA

Wani Mai Fafutuka Ya Rasu A Gidan Kurkukun Saudiyya

22:36 - March 12, 2018
Lambar Labari: 3482469
Bangaren kasa da kasa, Ali Jasem wani mai faftuka ne a kasar Saudiyya wanda ya rasa ransa a gidan kaso sakamakon azabtarwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kafofin yada labarai daban-daban sun tabbatar rasuwar Ali Jasem Nazaa mai fafutuka a kasar  Saudiyya a cikin kurkukun kasar.

A jiya mahukuntan na Saudiya sun sanar da mutuwarsa, amma sun ki yin wani Karin bayani kan dalilan rasuwar tasa,  kamar yadda kuma sun hana iyalansa da danginsa su ga gawarsa balantana a mika musu ita su yi mata jana’iza.

Wannan dai ba si ne karon farko da masarautar ‘ya’yan Saud take kashe masu fafutuka a kasar ba saboda dalilai na siyasa da kuma bangaranci na akida ko mazhaba.

Da dama daga cikin masu bin shafukan sada zumunta sun yi ta aikewada labarin rasuwar tasa, lamarin da ya daga hankulan al’ummomin yankin gabashin kasar.

Kasar Saudiyya dai tana daga cikin kasashen larabawa da suke bin salon tsarin sarautar kama karya kan al’ummominsu, tare da halaka duk wanda ya nuna rashin gamsuwarsa da salon mulkinsu.

3699107

 

 

 

 

 

captcha