IQNA

An Sanar Da Sunayen Wadanda Suka Lashe Gasar Kur’ani Ta Ajeriya

23:48 - June 12, 2018
Lambar Labari: 3482751
Bangaren kasa da kasa, an sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar kur’ani mai tsarki ta kasar Aljeriya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daren jiya an sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar kur’ani mai tsarki ta kasar Aljeriya, tare da gudanar da taron karshe na rufe gasar a babban masallacin Aljiers fadar mulkin kasar.

Ministan maa’ikatar addini ta Aljeriya Muhammad Isa ya sanar da cewa, Abdulaziz Shukri dan kasar Aljeriya ne ya zo na daya, Muhammad Haj As’ad daga Syria ya zo na biyu, Aiman bin Ahmad daga Tunis ya zo na uku.

Tun a ranar Talata da ta gabata ce dai aka fara gudanar da gasar, tare da halartar wakilan kasashe 53 na duniya, Muhammad Mahmudi shi ne ya wakilci kasar Iran a wannan gasa.

A daidai lokacin da ake gudana da wannan gasa ta duniya  akasar Aljeriya ne uma ake gudanar da wata gasar ta kur’ani amma ta kananan yara.

3722141

 

 

 

 

 

 

captcha