Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kananan yara da suke kasa da shekaru 15 da suka hada da maza da mata su 2780 suka gudanar da gasar.
An gudanar da gasr a bangarori hudu an harda, da suka hada da hardar dukkanin kur’ani, sai kuma rabin kur’ani da kuma hizib goma da hizib biyar.
Wasu daga jami’an gwamnati da suka hada da gwamnan lardin sharqiyyah da kuma wasu ‘yan majalisar dokokin kasar ta Masar sun halarci taron rufe gasar a jiya.