Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na akhbarelyom.com cewa, Mustafa Ragib wani fitacen mai koyar da yara karatun kur’ani n a lardin Kalyubiyya na Masar wanda ya rasu sakamakon bugun zuciya a jiya Asabar.
Bayanin ya ci gaba da cewa, Msatafa ya kasance sannane a bangaren kyar da kur’ani ga yara ‘yan makaranta, inda da dama suka koyi karau da harda a wajensa.
Ya yi karatu a bangaren ilimin addini a jami’ar Azhar ya saukyakkyawar sheda daga jama’aawan halayensa da son jama’a.
Ya rasu sakamakon bugun zuciya ba zato ba sammani, kuma a yau ne ake gudanar da janazarsa.