Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babbar asibitin Imam Zainul Abidin (AS) da ke birnin Karbala ta dauki nauyin yin hidima ta fuskar kiwon lafiya ga masu ziyarar Karbala lokacin Ashura kyauta.
Wannan na daga cikin irin ayyuka da cibiyoyin kiwon lafya masu zaman kansu suke gudanawa a wannan lokaci, inda dubban daruruwan mutane suke samun kulawa ta fuskar lafiya da magunguna kyata daga gae su.
Wannan cibiya ta sadaukar da dukkanin ayyukata a wannan lokaci ga al’umma masoya manzon Allah da ahlul bait da suke ziyaratr jikan manzon Allah (SAW) a hubbarensa.