IQNA

Ana Nuna Damuwa Kan Cin Zarafin 'Yan Adam A Bahrain

23:35 - September 21, 2018
Lambar Labari: 3483002
A zaman shekara-shekara na kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya da ake kammalawa yau, kasashe da dama sun nuna damuwa kan cin zarafin 'yan adam da mahukuntan Bahrain ke yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin jaridar yanar gizo ta Manama Post ya bayar da rahoton cewa, a zaman kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya da ake gunarwa a birnin Geneva na kasar Switzerland karo na talatin da tara, kasashe da dama sun nuna takaici matuka dangane da ake keta hurumin 'yan adam a kasar Bahrain.

Wakilan kasashe da suka hada da Ireland da Norway da kuma Danmark, sun kirayi gwamnatin kasar Bahrain da ta dakatar da cin zarafin 'yan adam da take yi, musammman ma wadanda take da sabani na mahangar siyasa da su da kuma kungiyoyin farar hula.

Wakilin Danmark ya ce dole ne Bahrain ta saki fursunonin siyasa da take tsare da su ba tare da wani dalili ba, daga ciki kuwa har da Abdulhadi Khawajah.

Tun a ranar Litinin da ta gabata ne aka fara gudanar da zaman taron, wanda za a kammala a yau Juma'a.

3748643

 

 

captcha