IQNA

Shirin Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Kasa A Najeriya

23:25 - December 03, 2018
Lambar Labari: 3483175
Bangaren kasa da kasa, an fara shirye-shiryen gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa baki daya a tarayyar Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, an fara gudanar da shirin gasar kur’ani ta kasa baki daya a Najeriya daga 28 ga Disamba zuwa 5 ga Janairu, wadda a wannan karon za a gudanar da ita ne a jahar Gombe da ke arewa maso gabashin kasar.

Sheikh Ibrahim shi ne mai kula da harkokin gasar kur’ani a jahar Edo, ya bayyana an gudanar da gasar share fage a jahar, wadda makaranta da mahardata 104 suka shiga, kuma daga cikinsu an fitar da mutane 60, daga cikinsu kuma aka zabi mutane 10 da za su wakilci jahar a gasa ta kasa.

A kowace shekara ana gudanar da gasar kur’ani a Najeriya tare da halartar wakilai daga dukkanin jahohin kasar.

3769124

 

 

 

captcha