IQNA

Taron Makon Kur’ani A Kasar Aljeriya

23:54 - December 04, 2018
Lambar Labari: 3483179
Bangaren kasada kasa, an fara gudanar da taron makon kur’ani mai tsarki a birnin Wahran nakasar Aljeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na amad ya habarta cewa, ma’aikatar kula da harkokin addinia  Aljeriya ta fara gudanar da tarukan makon kur’ani karo na ashirin.

Wannan taro na samun halartar malamai da jami’an gwamnati da kuma masana daga sassa na kasar, inda ake gabatar da jawabai dangane da lamarin kur’ani.

Baya ga haka kuma ana gudanar da karatutuka na kur’ani, inda makaranta da mahardata suke gudanar da gasa, daga karshe kuma a rufe da jawabin shugaban kasar.

Abdulazizi Butaflika yana yin amfani da wannan damar domin kara jawo hankalin al’ummar Aljeriya wajen ci gaba da yin riko da koyarwar kur’ani mai tsarki, da kuma rike amanar kasarsu da al’ummarta.

A wannan karon makaranta da mahardata 45 daga sassa na Aljeriya suke halartar babban taron na makon kur’ani mai tsarki karo na ashirina  kasar.

3769387

 

captcha