Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau jiragen yakin Saudiyya sun kaddamar da munana hare-harea kan yankin Shari'a Ts'in da ke cikin garin Al-shabab a cikin gundumar Alhudaiadah da ke yammacin kasar Yemen.
Rahoton ya ce a cikin 'yan kwanakin Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa da ke mara mata baya a yakin yemen, suna ci gaba da kaddamar da munanan hare-hare a kan birane daban-daban na kasar Yemen.
Wadannan hare-hare dai suna zuwa ne kwana daya kafin fara tattaunawa kan shirin zaman lafiya da sulhu a kasar ta Yemen a karkashin jagorancin majalisar dinkin duniya, wanda Saudiyya take nufin ganin ta rusa hakan ko ta wace hanya.
A nasu bangaren mayakan Ansarullah da aka fi sani da Huthi, da suke mara baya ga sojojin kasar masu yaki da mamayar Saudiyya sun sanar da cewa, an rattaba hannu kan wata yarjejeniyar musayar fursunoni a karkashin jagorancin kungiyar Red Cross.