IQNA

Wata Cibiyar Agaji A Canada Ta Bayar Da Dala Miliyan 100 Ga Yaran Rohingya

21:24 - December 07, 2018
Lambar Labari: 3483192
Wata cibiyar bayar da agaji da jin kai mai zaman kanta a kasar Canada ta bayar da dala miliyan 100 a matsayin taimako ga kananan yara 'yan kabilar Rohingya da kuma yaran Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai New Turk ya bayar da rahoton cewa, kungiyar bayar da agaji da jin kai ta LEGO da ke da baban mazauninta a kasar Canada, ta sanar da ware dala miliyan 100 a matsayin taimako ga kananan yara 'yan kabilar Rohingya da kuma yaran Syria da suke cikin mawuyacin hali.

Bayanin kungiyar ya ce wadannan kudin za a yi amfani da su ne domin sama ma yara na kabilar Rohingya da ke Myanmar ko kuma suke gudun hijira da kuma yara a Syria da yaki ya yi lahani abubuwan da suka fi bukata cikin gaggawa.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, za a fi mayar da hanali ne wajen yin amfani da kudin ga wadanda suke cikin mawuyacin hali na bukatar taimako, musamman marassa lafiya daga cikinsu, da kuma masu fama da matsalar abinci da wasu kayan bukatar rayuwa na larura.

An kafa kungiyar LEGO tun a cikin shekara ta 1986 a kasar Canada, kuma tana gudanar da harkokin kasuwanci inda a halin yanzu ta mallaki hannayen jari masu karfi a kamfanoni daban-daban na kasar da ma kasashen ketare, kuma tana amfani da ribar da take samu wajen taimakon marasa galihu.

3770238

 

 

 

captcha