Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na News 24 ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron kasar Afrika ta kudu sun bayar da bayanin cewa, a jiya Wasu 'yan bindiga sun harbe wani musulmi har lahira a kan hanyarsa ta zuwa masallaci domin yin sallar Juma'a, inda kuma suka ranta cikin na kare.
Jami'an 'yan sandan Afrika ta kudu sun ce lamarin ya faru ne a birnin Ekurhuleni da ke arewacin kasar a jiya da rana tsaka, kuma har yanzu ba a kame wadanda suka aikata wannan mummunan aiki ba, amma dai ana ci gaba da bin sawunsu da nufin cafke su.
Bayanin ya kara da cewa bayan harbin mutumin an dauke shi rai hannun Allah zuwa asibiti, amma saboda munanan raunukan da ya samu sakamakon shigar harsashia jikinsa ya rasa ransa.
Koa cikin watan Yunin wannan shekara wasu mutane sun kahe limamin wani masallaci a garin Cape Town tare da wasu daga cikin masallata.
Haka a cikin watan Mayun wannan shekara an kashe Abbas Essop limamamin masallacin Imam Hussain (AS) da ke garin Daurban, tare da gano wasu abubuwa masu fashewa da aka saka a cikin masallacin.