Jaridar Indepent ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, a jiya Juma'a kasa da sa'oi 24 da kai harin da aka yi a kan masallacin musulmia kasar New Zealand, wasu masu kyamar muslunci a birnin London na kasar Birtaniya sun kai farmaki da wukake a kan wani musulmi a lokacin da yake fitowa daga cikin wani masallacia birnin na Londin.
Rahoton ya ce mutane wasu ne uku daga cikin masu tsatsauran ra'ayin kin jinin musulmi a kasar ta Birtaniya suka kai harin a lokacin da aka kammala salla a cikin wani masallaci, inda suka biyu daga cikinsu suka nufi wani musulmi a lokacin da ya fito daga cikin masallacin suka yanke shi da wuka, inda suka yi masa munanan raunuka.
kafin zuwan jami'an tsaroa wurin mutanen sun tsere, kuma babu wani wanda aka kama daga cikinsu, amma jami'an 'yan sandan London sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin.