IQNA

Tawagogin Likotoci Na Kasashe 10 Suna Gudanar Da Ayyukan Lafiya A Taron Arbaeen

21:47 - October 18, 2019
Lambar Labari: 3484165
Bnagaren kasa da kasa, tawagar likitoci daga kasashe 10 suna gudanar da ayyukan lafiya a taron ziyarar arbaeen.

Kamfanin dillanicn labaran iqn aya bayar da rahoton cewa, Ahmad Jalil Al-shummari babban jami’i mai kula da ayyukan kiwon lafiya na hubbaren Imam Hussain ya bayyana cewa, akwai tawagar likitoci daga kasashe goma da suke gudanar da ayyukan lafiya a taron ziyarar arbaeen da ake gudanarwa.

Ya ce tawagogin sun fito ne daga kasashen Iran, Australia, India, Tanzania, Saudiyya, Bahrain, Pakistan, Kuwait, Lebanon da kuma Syria, inda suka kafa tantunansu a kusa da hubbaren Imam Hussain (AS).

Ya kara da cewa, hubbaren yana da asibitocin tafi da gidanka guda 35 da suke yin ayyuka na kula da lafiyar masu ziyara a ciki da wajen hubbaren, kamar yadda aka kafa wasu a kan manyan hanyoyin da ke isa Karbala daga biranan Bagdad, Babul da kuma Najaf.

Baya ga haka kuma Al-shammari ya bayyana cewa, babban asibitin Imam Zainul Abidin da ke birnin karbala ma yana gudanar da ayyuka sa’oi 24 kyauta ga masu ziyarar arbaeen.

 

3850357

 

 

 

captcha