IQNA

Cibiyoyi Da Kungiyoyin Agaji Na Duniya Na Kai Taimako Ga Al’ummar Falastinu

22:13 - May 18, 2021
Lambar Labari: 3485927
Tehran (IQNA) Kungiyoyin agaji na duniya suna tattara taimako ga al’ummar Falastinu da ke fuskantar kisan kiyashi daga yahudawan Sahyuniya.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar, ma’aikatar kiwon lafiya ta Falastinu ta sanar da cewa, duk da luguden wutar da Isra’ila yake yi a kan al’ummar yankin zirin Gaza, amma wasu kungiyoyin agaji suna aikewa da taimako na kayayyakin bukatar rayuwa ga al’ummar yankin.

The Middle East Children’s Alliance wato MECA a takaice, ta aike da wasu kayayyakin tallafi da ta tattara, da suka hada kayan abinci da wasu kayayyakin bukatar rayuwa musamman na kananan yara, wanda kuma an aike da wasu daga cikinsu zuwa Gaza.

Cibiyoyi Da Kungiyoyin Agaji Na Duniya Na Kai Taimako Ga Al’ummar Falastinu

Ita ma a nata bangaren kungiyar bayar da agaji da tallafi ga yara Falastinawa ta Palestine Children’s Relief Fund, ta aike da wasu kayan agaji da taimako ga al’ummar yankin zirin Gaza.

Cibiyoyi Da Kungiyoyin Agaji Na Duniya Na Kai Taimako Ga Al’ummar Falastinu

Baya ga haka kuma wasu kungiyoyin da cibiyoyin daban-daban da suka hada da Medical Aid for Palestinians, Muslim Aid USA, The Institute for Middle East Understanding da suke a kasar Amurka, su ma suna aikewa da nasu taimakon, sanann suan ci gaba da tattara abin da ya sawaka domin ganin cewa sun taimaka ma Falastinawa, sakamakon mawuyacin halin da Isra’ila ta jefa su.

Cibiyoyi Da Kungiyoyin Agaji Na Duniya Na Kai Taimako Ga Al’ummar Falastinu

Cibiyoyi Da Kungiyoyin Agaji Na Duniya Na Kai Taimako Ga Al’ummar Falastinu

3972044

captcha