IQNA

Jagoran Juyi Na Iran: Ranar Zabe A Iran Ranar Fayyace Makomar Kasa Ce

20:52 - June 18, 2021
Lambar Labari: 3486023
Tehran (IQNA) A safiyar yau Juma’a 18 ga watan Yunin 2021 ne aka fara kaɗa kuri’a a zaɓen shugaban ƙasa karo na 13 a duk faɗin ƙasar Iran bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kaɗa kuri’arsa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kaɗa kuri’ar tasa ne a Husainiyar Imam Khomeini da ke gidansa tun da misali ƙarfe 7 na safiya kamar yadda aka tsara.

Jim kaɗan bayan kaɗa kuri’ar tasa a akwatunan da aka tanadar don zaɓen shugaban ƙasa, zaɓen ‘yan majalisar jihohi da ƙananan hukumomi da kuma zaɓen cike gurbi na majalisar ƙwararru ta jagoranci, Imam Khamenei ya gabatar da ɗan gajeren jawabi a matsayin amsa ga tambayar da ɗan jaridar hukumar gidan radiyo da talabijin na Iran ya yi masa.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar fitowar jama’a don kaɗa kuri’arsu lamari ne da zai amfani ƙasa da kuma tabbatar da tsaronsu yana mai cewa kaɗa kuri’ar jama’a a yayin wannan zaɓen wani lamari ne mai ayyana makomarsu.

Har ila yau kuma Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi al’ummar Iran ɗin da su fito kwansu da ƙwarƙwatarsu don kaɗa kuri’arsu a wannan zaɓen saboda muhimmancin da hakan yake da shi ga makomar ƙasar da kuma juyin juya halin Musulunci na ƙasar, yana mai kiran al’ummar da cewa su fito su yi hakan tun da wurwuri kada su bari sai lokaci ya ƙure.

Yayin da yake magana kan muhimmancin da kuri’ar kowane ɗan ƙasa take da shi kuwa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewa duk da cewa kuri’ar guda kowane mutum yake da ita, amma lalle wannnan kuri’ar tana da muhimmanci.

Daga ƙarshe dai Jagoran ya gode wa dukkanin jami’ai da ma’aikatan da suke gudanar da ayyukan zaɓen kamar yadda kuma ya kiraye su da su yi aikin su da kyau, haka nan kuma ya gode wa ‘yan jaridar da suka zo don shirya rahotanni kan zaben.

A yau Juma’ar dai ana gudanar da zaɓuɓɓuka uku ne a ƙasar ta Iran da suka haɗa da zaɓen shugaban ƙasa, zaɓen ‘yan majalisar jihohi da ƙananan hukumomi da kuma zaɓen cike gurbi na majalisar ƙwararru ta jagoranci.

A zaɓen shugaban ƙasar dai, yan takara 4 ne suke fafatawa a tsakaninsu da suka haɗa Sayyid Ibrahim Ra’isi, Abdul Nasir Hemmati, Muhsin Rizae da kuma Amir Husain Qadhizadeh Hashemi.

3978228

 

captcha