Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, kwamandan ‘yan sintiri na jihar Kebbin da ke arewa maso yammacin Najeriya, Umar Hussaini Rambo, ya ce rashin daukar mataki daga gwamnati ne, ya tilasta wa mutanen garin yin fito-na-fito da ‘yan bindigar.
Daya daga cikin daliban kwalejin Yaurin ya rasa ransa sakamakon musayar wuya tsakanin sojoji da ‘yan bindigar da suka sace daliban.
Mataimakin Kwamandan Rundunar Hadin-Guiwa a yankin a shiyar arewa maso yammacin Najeriya, Air Commodore Abubakar AbdulKadir ya tabbatar da musayar wutar da aka yi tsakanin bangarorin biyu a yayin zantawarsa da manema labarai a Zamfara.
Jami’in ya cewa, an kuma yi nasarar kubutar da dalibai hudu da malami guda daga hannun ‘yan bindigar.
‘Yan sandan jihar Kebbi sun bayyana cewa, ana ci gaba da aiki tukuru da zummar kubutar da sauran daliban da ‘yan bindigar suka sace a ranar Alhamis.
Har yanzu ba a tantance hakikanin adadin daliban da ‘yan bindigar suka sace ba daga makarantarsu.