A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, dakin ajiyar kayan tarihi na Pergamon a birnin Berlin na kasar Jamus, wuri ne da ake ajiyar kayan tarihi na al'ummomi daban-daban na duniya.
Kayan tarihi na al'ummomin musulmi daga kasashe daban-daban na daga cikin kayayyakin da ake ajiye da su a wannan wuri, wanda fiye da mutane miliyan daya ke ziyartar wurin a kowace shekara, domin ganewa idanunsu abubuwan da ake ajiye da su a wurin.