IQNA

Nasrullah Ya Aike Da Sako Na Musamman Ga Zababben shugaban Iran Ibrahim Ra'isi

21:52 - June 21, 2021
Lambar Labari: 3486035
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya aike da sakon taya murnar lashe zaben shugaban kasa zuwa ga Sayyid Ibrahim Ra’isi.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a cikin sakon da Sayyid Nasrullah ya aike wa zababben shugaban kasar Iran ya bayyana cewa, dukkanin masu gwagwarmaya da zaluncin yahudawan sahyuniya da kasashe masu girman kai ‘yan mulkin mallaka, suna da kyakkyawar fata a kan zababben shugaban na Iran.

Sannan kuma Sayyid Nasrullah ya taya Ra’isi murnar samun nasarar lashe zaben shugaban kasar ta Iran da aka gudanar, tare da yi masa fatan samun nasara da taimako daga Allah wajen gudanar da shugabanci na gari.

Tun bayan sanar da Ra’isi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Iran a ranar Asabar da ta gabata, yake ci gaba da samun sakonnin taya murna daga shugabannin kasashen duniya, da kuma manyan ‘yan siyasa da fitattun mutane daga ko’ina cikin fadin duniya.

Mutane miliyan 28 da 933,004 ne suka kada kuri’unsu a zaben na kasar Iran, daga cikin mutane miliyan 59 da 310,307 da suka cancanci kada kuri’a a kasar, wato kashi 48.8% na dukaknin wadanda suka cancanci kada kuri’a a kasar ta Iran ne, suka kada kuri'unsu a wannan zabe.

Raeisi ya samu kuri’u miliyan 17, da 926,345 daga cikin kuri’un da aka kada, yayin da Mohsen Reza’i ya samu miliyan 3 da 412,712, sai kuma Abdulnasir Hemmati miliyan 2 da 427,201, sai kuma Amir HussainQadi Zadeh Hashemi, wanda ya samu kuri’u 999,718, yayin da sauran kuri’u miliyan 3 da 726,870 batattu ne.

 

captcha