Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan gasa ta fara ne a ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamba, inda kuma masu karatu daga kasashe 20 da suka hada da Rasha, Bahrain, Yemen, Masar, Morocco, Turkiya, UAE, Sudan, kungiyar kasashen renon Ingila da kuma Syria suka halarci gasar.
Bayan sanar da sakamakon wadannan gasa a wajen rufe gasar, Ahmed Kozo daga Turkiyya ne ya zo na daya, Abd al-Rahman Faraj daga Masar ya zo na biyu, Seyed Mustafa Hosseini ya zo na uku, sai Qari daga Yemen ya zo na hudu.
A cikin shirin za ku ga bidiyon karatun fitaccen malamin nan na Iran Sayyid Mostafa Hosseini a wajen bikin rufe wannan gasar kur'ani ta kasar Rasha.
An gudanar da wannan gasa ne bayan shafe tsawon shekaru biyu ana fama da annobar Corona, kuma an kammala a yau tare da halartar jakadun kasashen musulmi da Sheikh Ravil Ainuddin shugaban majalisar Mufti na kasar Rasha.