IQNA

An Bukaci Azahar Da Ta Taimaka Wajen Rubuta Kur'ani A Burnei

21:59 - August 13, 2014
Lambar Labari: 1439208
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin daliban jami'ar Burnei da suke gudanar da ayyuka na bincike dangane da lamurran addini sun bukaci jami'ar Azhar da ta taimaka musu wajen gudanar da wani aiki da suke yin a rubutun kur'ani mai tsarki.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na yaum Sabi cewa, wasu daga cikin daliban jami'ar Burnei da suke gudanar da ayyuka na bincike dangane da lamurran addini sun bukaci jami'ar Azhar da ta taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu na rubutun kur'ani mai tsarki da suka fara.

Wannan kira ya zo ne a lokacin daliban suke gudanar da wata ziyara ta musamman a babban ginin cibiyar Azahar da ke birnin Alkahira na kasar Masar, inda suka gana da wasu daga cikin fitattun malaman cibiytar, da suka hada hard a babban malamin jami'ar Dr Ahmad Tayyib.

Yanzu haka dai a cewar daliban aikin nasu ya yi nisa wajen rubutun, amma kuma hakan aiki ne da bukatar manyan malamai su sanya hannu domin tabbatar da cewa komai yana tafiya yadda ya kamata bisa, domin kuwa rubutun kur'ani lamari mai matukar muhmmanci.

Kasar Burnei dai tana yankin gabacin Asia ne, kuma mutanen kasar kimanin kashi 67 daga cikin mabiya addinin muslunci ne, sai kashi 13 mabiya addinin Buda, kasji 10 kuma kiristoci, wasu 10 kuma mabiya wasu akidu na daban.

1438663

Abubuwan Da Ya Shafa: burnei
captcha