IQNA

‘Yan Shi’a A Kasar saudiyyah Sun Yi Allawadai Da Harin Da Aka Kai Kan Jami’an Tsaron Kasar

23:55 - August 08, 2015
Lambar Labari: 3340242
Bangaren kasa da kasa, mabiya mazhabar shi’a na kasar Saudiyya da ke zaune a yankin Ihsa na kasar sun yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai jami’an tsaron kasar da ke yankin Abha a kudancin kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwatan cewa, a cikin wani bayani da suka fitar mabiya mazhabar shi’a na kasar Saudiyya da ke zaune a yankin Ihsa na kasar sun yi Allawadai da harin ta’addancin da aka kai jami’an tsaron kasar da ke yankin Abha a kudancin kasar a ranar Alhamis da ta gabata.

A ranar laraba da ta gabata ce aka kaddamar da wani harin kunar bakin wake a wani masallaci da ke a wani wurin tsaro a garin Abha da ke cikin gundumar Asir a kudancin Saudiyyah, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17, akasarinsu jami’an tsaro.

Jim kadan bayan kai harin kungiyar IS mai dawa’ar jihadi ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin kai harin, kuma ta sha alwashin ci gaba da kaddamar da hare-hare makamantan hakan a cikin kasar ta Saudiyya.

A cikin watan Mayun da ya gabata an kai wasu hare-hare makamantan hakan a wasu masallatan Juma’a a yankunan gabacin kasar ta Saudiyya, wadanda akasarin mazauna wadana yankuna mabiya mazhabar shi’a ne, inda aka kashe tare da jikkata mutane da dama.

Harin yay i sanadiyyar mutuwar mutane 15 tare da jikkatar wasu kimanin 20, tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin Saudiyya ta nuna damuwa dangane da yadda matasan kasar suke shiga cikin kungiyoyin ta’addanci fiye da sauran matasa na kasashen larabawa, inda su ne suka fi yawa a cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasashen larabawa, inda a halin yanzu sun samu horo da gogewa kan kidan bil adama, kuma wasu daga cikinsu sun koma kasar ta Saudiyya.

Wannan ne yasa babban mai bayar da fatawa a masarautar Al-Saud ya haramta wa samarin Saudiyyah zuwa kasashen Syria da Iraki domin yin jihadi, bisa hujjar cewa za su iya haifar da matsalar tsaro idan suka komo gida, duk kuwa da cewa bai haramta yin hakan ga sauran samari na kasashen larabawa da ma na sauran kasashen duniya ba.

3340060

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyyah
captcha