IQNA

Martanin Babban Mai Bayar Da fatawa Ga Wahabiyawa kan Fin Din Muhammad Rasulullah (SAW)

23:34 - September 02, 2015
Lambar Labari: 3357561
Bangaren kasa da kasa, bababn mai bayar da fatawa ga wahabiyawan Saudiyyah ya bayyana cewa cewa din Muhammad Rasulullah (SAW) da Majid Majidi dan kasar Iran ya yi fim ne na fasikanci da kauce ma musulunci.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-alam cewa, babban mai bayar da fatawa ga wahabiyan Saudiyya Abdulaziz Al Sheikh ya bayyana cewa, fin din Muhammad Rasulullah na majusanci kuma yaharamta a kale shi a shar’ance a mahangarsa ko kuma yada yada shi.

Mutumin ya ci gaba da cewa an siffofin manzon Allah kuma shi ya tsarkaka daga bayyana shi a cikin sura ta fim, saboda haka Iraniyawa suna son su fitar da wani abu ne domin su yi izgili ga manzon Allah ta hanyar suranta shia  cikin fim, wanda kuma a cewarsa yin hakan aiki ne na fasiknci.

Jaridar Alhayat ta rubuta cewa, mai bayar da fatawa ga wahabiyawan Saudiyya ya bayyana cewa, kallon fim ya haramta haka nan kuma yada shia  zuwa ga wasu mutane na daban, a kan haka yana gargadin mabiyansu da su yi hattara kan hakan.

Duk da cewa masana kan tarihi daga ko’ina cikin fadin duniya musulmi sun yi na’am da wannan fim na Majid Majidi, amma malaman wahabiyawan Saudiyya tun a watannin da suka gabata suke ta sukar lamarin, bisa hujjar cewa dukkanin wadanda suka shirya fim din Iraniyawa.

3357354

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyyah
captcha