IQNA

Netanyahu Ya Bayana Farin Cikinsa Kan Hana Iran Zuwa Aikin Hajji

15:53 - September 16, 2016
Lambar Labari: 3480785
Bangaren kasa da kasa, firayi ministan haramtaccyar kasa Isra’ila Ben jamin etanyahu ya bayyana farin cikinsa kan hana musulmin Iran zuwa aikin hajjin bana.
Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alalam cewa, Netanyahu a lokacin da yake zanatawa da jaridar Isra’ila ta Times of Israel ya bayyana farin cikinsa kan hana muuslmin Iran zuwa aikin hajji.

Yace ko shakka baba bin da ya faru na daukar matakin hana Iraniwa zuwa aikin hajji abin farin ciki ne ga Isra’ila, kuma a cewarsa ba za su boye farin cikinsu ba kan hakan, domin kuwa Iran ita ce babbar makiya ga Isra’ila.

Bayan nan kuma ya kirayi sauran kasashen larabawa da su koyi da Saudiyyah kan irin wanan mataki da Sadiyya take dauka a kan kasar Iran saboda acewarsa Iran itace babbar makiya gare su baki daya.

Netanyahu ya kara cewa daukar irin wannan mataki zai kara taimakawa wajen kyautata alaka tsakanin Isra’ila da kasashen larabawa tare da mayar da Iran saniyar ware.

Tun kafin wannan lokacin dai mahukuntan Iran sun bayyana matakin hakna musulmin kasar Iran zuwa hajji da cewa ba lamari ne da ke hannun yayan Saud ba, umarni ne daga iyayen gidansu yahudawan Isra’ila wand aba za su iya saba mas aba.

3530422


captcha