IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Gina Wani Rami A Gefen Masallacin Aqsa

21:44 - December 28, 2016
Lambar Labari: 3481077
Bangaren kasa da kasa, ministan al’adu na Isra’ila ya ce sun gina wani ramin karkashin kasa da ya hada Wadil Hulwa da kuma Babul Magariba da ke gefen masallacin Aqsa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Mashriq ya naklato daga jaridar Quds Al-arabi cewa, ministan na Isra’ila Mary Ragif ya bayyana cewa, an kaddamar da bude wannan rami cikin nasara.

Kafin lokacin dai haramtacciyar kasar Isra’ila ta jibge darurwan ‘yan sanda a cikin kayan sarki domin tabbatar da cewa Palastinawa mazauna birnin quds ba su cikas ga wannan shiri ba.

Kwamitin da ke kula da masallacin quds ya sanar da cewa tun kimanin shekaru biyu da suka gabata ne gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila ta fara wannana iki, inda ta rarake bangaren kudancin masallacin aqsa da kuma gidajen Palastinawa da ke wurin, wanda a kowane lokaci wurin zai iya ruftawa.

Palastinawa da dama mazauna gabashin birnin Quds sun ce wannan fafakeken rai da Isra’ila ta yi ya cutar da gidajensu, inda yanzu haka wasu gidajen sun manyan tsagogi, yayin da katangar masallacin Quds a kudancin masallacin take tsaye a kan ramukan, inda za ta iya faduwa a kowane lokaci.

A cikin wannan makon ne yahdawan za su gudanar da idinsu na Hanuka, inda za su gudanar da tarukansu a cikin masallacin quds mai alfarma, tare da halartar manyan jami’an gwamnatin Netanyahu da ‘yan majalisar Kneset da sauran yahudawa masu tsatsauran ra’ayi.

3557377


captcha