IQNA

An Kaddamar da Hasumiyyar Kiran Salla Mafi Tsawo A Quds

23:42 - March 18, 2017
Lambar Labari: 3481324
Bangaren kasa da kasa, an kaddamar da hasumiyar kiran salla mafi tsawo a yankin Isawiyyah da ke cikin birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sheikh Ikrama Sabri babban limamin masallacin Quds shi ne ya jagoranci kaddamar da wannan hasumiya a wani masallaci da ke yankin Al-isawiyyah.

Ya ce an gabatar da aikin wannan hasumiyya ne tare da hadin gwiwa da sauran al’ummar yanki, wadanda ya ce hakika sun yi kokari wajen ganin an cimma wannan buri.

Haka nan kuma ya bayyana hakan a matsayin martanin al’ummar quds kan dokar hana kiran salla da mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila suka kafa, tare da jinjina wa larabawa da suke zaune a cikin yankunan da Isra’ila ta mamaye tun a cikin shekara ta 1948.

3584951

captcha