IQNA

Qasemi: Tuhumce-Tuhumcen Saudiyya Kan Iran Ba Su Da Tushe

16:29 - November 06, 2017
Lambar Labari: 3482071
Bangaren kasa da kasa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana tuhumce-tuhumcen gwamnatin Saudiyya a kan Iran da cewa ba su da tushe balantana makama.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ta bakin mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, ta yi watsi da tuhumce-tuhumcen Sa'ad Hariri, tsohon firayi ministan Labanon mai murabus, tana mai cewa maganganun nasa sun yi daidai da tuhumce-tuhumce marasa tushe da Amurka da Sahyoniyawa da Saudiyya suke yi da nufin haifar da sabon rikici a kasar Labanon da kuma yankin Gabas ta tsakiya.

Bahram Qassemi ya ce: Murabus ba shiri da Haririn da kuma sanar da hakan daga wata kasa ta waje ba wai kawai abin bakin ciki da mamaki ba ne, face dai wata alama ce da take nuni da cewa yana rawa ne da bazan masu fatan sharri ga wannan yanki".

A cikin jawabin murabus din na sa, Hariri ya zargi Iran da Hizbullah da tsoma baki cikin harkokin kasashen larabawa da haifar da fitina.

A daya bangare kuma Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran,Bahram Qassemi, ya ce a daidai lokacin da ake daf da murkushe kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh a wasu kasashen yankin, kamata ya yi a guji duk wasu kalamai dake iya tada fitina, a kuma nemi hanyoyin gina kasashen da 'yan ta'adda suka ruguza.

A jiya Asabar ne dai firayi ministankasar Lebanon Sa'ad Hariri ya sanar da yin murabus daga kan mukaminsa a lokacin da yake gudanar da ziyarar aiki a kasar Saudiyya bayan ya yi zargin cewa yana fuskantar barazanar kisan gilla.

3660739


captcha