IQNA

Kungiyar Kare Dimukradiyya Ta Duniya Ta Allah Wadai Da Masarautar Kama Karya Ta Bahrain

23:55 - February 03, 2018
Lambar Labari: 3482362
Bangaren kasa da kasa, babbar kungiyar kare dimukradyya ta duniya ta yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da matakan zalunci da masarautar kamar karya take dauka kan ‘yan adawar siyasa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Lu’lu’a ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayani da ta fitar a yau babbar kungiyar kare dimukradyya ta duniya ta yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da matakan zalunci da masarautar kamar karya take dauka kan ‘yan adawar siyasa ta hanyar kama su tare da yanke musu hukunci a kotun soja.

A cikin wannan makon ne kotun sojin masarautar kama karya ta Bahrain ta yanke hukuncin kisa da kuma dauria gidan kaso a kan wasu masu adawa ta siyasa a kasar.

Kotun ta  yanke hukuncin kisa a kan mutane 2, wasu 19 kuma daurin rai da rai, wasu 17 shekaru 15 a gidan kaso, 9 kuma daurin shekaru 10, wasu 11 kuma shekaru 5, yayin da 47 daga cikin an janye musu hakkinsu na zama ‘yan kasa.

Kungiyar kare dimukradiya ta duniya ta ce wannan ba abu ne da za a yi shiru a kansa ba, tun da manyan kasashen duniya sun yi gum da bakunansu kan irin wannan mummunan zalunci da masarautar kama karya ta Bahrain take tafkawa kan fararen hula na kasar, saboda dalilai na siyasa ko kuma na banbancin akida.

‘Yan tsiraru wahabiyawa da turawan Birtaniya suka mika wa ragamar mulkin kasar a lokacin mulkin mallaka, su ne suke ci gaba da shugabancin kasar karkashin kulawar Birtaniya da kuma saumun dauki daga masarautar wahabiyawa ta Alu Saud gami da Amurka da kuma haramtacciyar gwamnatin yahudawa.

3687734

 

 

 

 

 

captcha