IQNA

An Girmama Wasu Mutane Da Suka Yi Bincike Da Rubutu Kan Imam

23:04 - February 04, 2018
Lambar Labari: 3482363
Bangaren kasa da kasa, an girmama wasu mutane da suka gudanar da bincike da kuma rubutu kan marigayi Imam Khomenei (RA) a kasar Senegal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sayyid Hassan Ismati shugaban karamin ofishin jakadanin kasar Iran a Senegal ya jagoranci wani taron girmama wasu mutane da suka gudanar da bincike da kuma rubutu kan marigayi Imam Khomenei (RA) a kasar, tare da basu kyautuka na musamman.

Daga cikina bin da aka yi har da bayar da kyautuka na kudade da kuma littafai ga mutane hamsin wadanda suka fi nuna kwazo wajen yin bincike da kuma rubutu kan rayuwar Imam Khomenei (RA) da gwagwarmayarsa da kuma fadi tashin da ya yi wajen neman ilimi.

Makalolin da aka rubuta suna a matsayin wani abun alfahari ga al'ummar kasar Iran, musamman ganin cewa dukkanin wadanda suka yi rubutun babu wani ba'iraniye a cikinsu, dukkaninsu mutanen kasar Senegal ne, amma sun iya bayyana abubuwa masu matukar muhimmanci a cikin rayuwarsa.

Daga karshe an yi addu'a ga Imam Imam kuma marigayi sheikh Toure tsohon shugaban darikar muridiya a kasar ta Senegal.

3688430

 

captcha