IQNA

Matashi Dan Kasar Masar Mai Burin Yin Kiran Salla A Haramin Makka

23:16 - March 10, 2018
1
Lambar Labari: 3482465
Bangaren kasa kasa, Mahmud Fadel matashi dan kasar Masar mahardacin kur’ani da yake da burin yin kiran salla a cikin haramin Makka mai alfarma.

Matashi Dan Kasar Masar Mai Burin Yin Kiran Salla A Haramin MakkaKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shain sadarwa na yanar gizo na almisriyun cewa, Mahmud Fadel matashi dan kasar Masar mahardacin kur’ani ne wanda kuma da yake da babba burin ganin ya yi kiran salla a cikin haramin Makka mai alfarma da yakkyawan sautinsa.

A zantawarsa da tashar talabijin ta DMC, ya bayyana cewa, har kullum babban burina shi ne a duk lokacin da na samu damar ardace kur’ani in yi kiran salla a cikin haramin Makka, shi ne abin da na ke fata yanzu.

Muhammad Fadel yana karatu a jami’ar Halwan a bangaren harkokin asuwanci.

Muhammad Tablawi shugaban kungiyar hadin kan mahardatan kur’ani ta kasar Masar ya sheda masa cewa lallai sautinsa yana da kyau.

3698492

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
allah ya cika nufi
captcha