IQNA

Limamin Juma’a A Tehran: Albarkacin Juyin Musulunci Ne Iran Ta Yi Tsayin Daka A Gaban Amurka

23:52 - June 01, 2018
Lambar Labari: 3482714
Bangaren siyasa, Na'ibin limamin masallacin juma'ar Tehran Hujjatul Islam Sayyid Mohammad Hassan Abuturabi Fard ya bayyana cewa gungun kasashe da kungiyoyin masu fada da zalunci a yankin gabas ta tsakiya suna kara karfi sosai a yankin.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hullatul Islam walmuslimin Sayyid Muhammad Hassan Abuturabi fard ya bayyana haka ne a cikin hudubobin na sallar Jumma'a a nan birnin Tehran.

Ya kuma kara da cewa dakaru "mukawama" a kasashen Siriya, Lebanon, Palasdin da Yemen duk, Alhamdu lillah -suna samun nasarori a gwagwarmayan da suke yi da azzalumai kasashen yankin da kuma girman kan Amurka.

Turabi ya kara da cewa hadakan da wadanan kasashe ko kungiyoyi suke yi da JMI sannan karkashin jagorancin Jagoran juyin juya halin musulunci Aya.

Sayyid Aliy Khamenei ya sa suna samun nasarori a kan makiyansu a cikin yan kwanakin nan.

Sannan yake yaken wakilci wanda magoya bayan Amurka da kawayensu suke gudanar da su a yankin suna kara cin baya a duk ranar Allah.

Na'ibin limamin masallacin jumma'a a nan Tehran ya kammala da cewa yunkurin 15 ga watan Khordad na shekara ta 1342 wanda mutanen kasar Iran suka yi, karkashin jagorancin marigayi Imam Khomaini (qs) ya zama babban milsali ga dukkan masu gwagwarmaya a yankin da kuma duniya gaba daya.

3719484

 

 

captcha