IQNA

Qasemi: Harin Ta’addancin Afghanistan Na Tabbatar Da Dabbancin Maharan

23:27 - June 05, 2018
Lambar Labari: 3482727
Bangaren kasa da kasa, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya yi tofin Allah tsine kan harin ta'addancin da aka kai wajen zaman taron malaman addinin Musulunci a kasar Afganistan.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Bahroum Qasimi a jiya Litinin ya gabatar da juyayi da alhinin kasar Iran ga gwamnatin Afganistan da al'ummar kasar musamman iyalan mutanen da suka rasa rayukansu ko suka jikkata sakamakon harin ta'addancin da aka kai kan zaman taron malaman addinin Musulunci a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afganistan a jiya Litinin.

Bahroum Qasimi ya kara da cewa: Manufar 'yan ta'adda ita ce kokari ganin sun hana duk wani kokarin wayar da kan al'umma kan hakikanin koyarwar addinin Musulunci da fayyace matsayin addinin na Musulunci kan zaman lafiya da sulhu gami da mutunta hakkin dan Adam da kuma irin gagarumar rawar da malaman addinin Musulunci zasu taka a fagen wayar da kan al'umma domin bunkasa ci gaban rayuwa.

A jiya Litinin ce wani dan ina ga kisa da yayi jigida da bama-bamai ya tsarwatsa kansa a wajen zaman taron daruruwan malaman addinin Musulunci na kasar Afganistan kan neman hanyar shawo kan amfani da Musulunci a fagen ayyukan ta'addanci musamman fitar da fatawowi kan kafirta musulmi tare da halatta jininsu da ma na sauran mabiya addinai, inda harin ya lashe rayukan mutane akalla bakwai tare da jikkata wasu tara na daban. 

3720462

 

captcha