IQNA

An Cimma Yarjejeniyar Dakatar Bude Wuta Tsakanin Isra’ila da Falastinawa

23:45 - May 06, 2019
Lambar Labari: 3483613
Bangaren kasa da kasa, kakakin kungiyar ajbhar dimukradiyya a Falastinu ya sanar da cewa an cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin bangaren Isra’ila da Falastinawa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, tashar talabijin ta Alnmayadeen ta bayar da rahoton cewa, Hukumonin Palasdinu sun amince da tsagita wuta da yahudawan mamaya na Isra’ila, bayan shafe kwanai biyu na barin wuta a tsakaninsu.

Wasu majiyoyi daga jami’an Palasdinawan a Gaza, sun bayyana wa masu aiko da rahotanni cewa sun amince tsagaita wuta bayan wani shiga tsakani na kasar Masar.

A cewar wasu majiyoyi daga kungiyar Hasas da kuma ta gwagwarmayar musulinci, shirin tsagaita wutar ya fara aiki daga karfe hudu da rabi na daren jiya.

Ko baya ga hakan akwai wata majiya daga hukumomin masar data tabbatar da labarain, saidai har kawo lokacin fasara wadannan labaran, hukumomin yahudawan na Isra’ila basu ce uffan ba kan batun.

Rikicin tsakanin bangarorin biyu ya dada kazancewa a kwanaki biyu nan, yayin da Falasdinawan sukayi wa Isra’ila ruwan rokoki sama da 450, ita kuwa Isra’ila ta kai hare haren jiragen sama 200, a Gaza, inda Palasdinawa 19 suka rasa rayukansu.

Daga bangaren Israi’la an rawaito mutuwar mutane hudu tare da jikkatar wasu da dama, inda wasusu suke kwancea a asibiti.

3809250

 

 

captcha