IQNA

Kafar Sadarwa Ta Zumunta Facebook Na Shirin Shafukan Cin Zarafin Musulunci

17:00 - February 03, 2015
Lambar Labari: 2804013
Bangaren kasa da kasa, shafin sadarwa na zumunta na facebook na shirin daukar wani kwakwaran mataki na rufe dukkanin shafikan da ke cin zarafin addinin muslunci ta wannan kafa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Top Conservative News cewa, shafin facebook na shirin daukar wani kwakwaran mataki na rufe dukkanin shafikan da ke cin zarafin addinin muslunci a hanyoyin da yake ta yanar gizo.
Wasu daga cikin matasa kasar Morocco ne suka fara daukar wannan mataki da suke aiki tare da shafin, inda a halin yanzu reshen wannan kafa da yake a kasar zai fara daukar wannan mataki domin dakile duk wani yunkuri na masu neman shafa wa addinin muslunci kashin kaji ta wanann hanya.
Shafin dai ya sanar da hakan bayan da suka fara kai ruwa tare da wata kotu a kasar Turkiya, wadda ta ce za ta yi shari’a kan saka batutuwa na cin zarafi da kuma batunci ga manzon Allah tsora da amincin Allahs u tabbata a gare shi da ake sakawa a cikin wannan shafi na sada zumunta.
Kotun ta ce ta shirya tsaf domin yin shari kan wannan batu matukar dai shafin bai dauki wani kwakwaran matakai na dakile yin hakan ba, kamar su kansu mahukunta  akasar Turkiya suka ce za su rufe shafin baki daya  akasar, matukar ba adaina yin batunci ga addinin muslunci da kuma manzon rahama ba.
2802754

Abubuwan Da Ya Shafa: shafi
captcha