Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei dangane da barazanar da wasu jami’an Amurka biyu suka yi kan Iran ya bayyana cewa, tattaunawa karkashin barazana ba ta da wata ma’ana, Iran ba za ta amince da haka ba.
2015 May 07 , 20:25
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin juya halin muslunci a lokacin ganawarsa da manyan jami’an soji da kuma na ma’aikatar tsaro a yau ya bayyana cewa, dole ne a kara mayar da himma wajen bunkasa ayyukan tsaro da kare kasa domin zama cikin shiri da fusantar kowane irin kalu bale.
2015 Apr 19 , 23:20
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jadda cewa dole ne a janye dukkanin takunkuman da aka dora wa jamhuriyar muslunci daga lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar karshe, wannan lamari ne mai matukar muhimmanci da ba za a yi saku-saku da shi ba.
2015 Apr 10 , 23:37
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khameenei jagoran juyin juya halin muslunci a Iran,a lokacin da yake gabatar da jawabi a haramin Imam Rida (AS) a gaba dubban daruruwan mutane ya bayyana cewa, bisa la’akari da kalubale da ke gaban gwamnati wajibi ne a kan kowa daga cikin al’umma ya yi abin zai iya domin bayar da tasa gudunmawa.
2015 Mar 22 , 23:21
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya taya al'ummar Iran da sauran al'ummomi da ke amfani da shekarar shamsiyya, murnar idin Nourouz da kuma shiga sabuwar shekarar shasiyyah ta 1394.
2015 Mar 21 , 23:09
Bangaren siyasa, ya zama dole a mu canja barazaran da ake yi ta kyamar musulmi da bayyana musulunci na gaskiya, mu bayyana banbancinsa da akidar watsi da addini, rahamarsa ga raunana, jihadinsa a kan masu girman kai, ta haka za mu hana makiya samun damar kawar da hankulan duniya daga muslunci na gaskiya.
2015 Mar 12 , 22:36
Bangaren siyasa, masoya manzon Allah daga koina cikin fadin jamhuriyar musulunci sun taru domin nuna goyon bayansu ga manzo da kuma juyin juya hali.
2015 Feb 11 , 20:46
Bangaren siyasa, A safiyar yau Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya gana da kwamandoji da jami'an rundunar sojin sama da dakarun kare sararin samaniyya na Iran, inda y ace ranar 22 ga watan bahman rana ce da makiya za su sha kunya.
2015 Feb 08 , 21:08
Bangaren kasa da kasa, Jagoran juyin juya halin musulunci ya aike da wata wasika da aka rubuta a cikin harshen turancin zuwa ga matasan nahiyar turai da kuma arewacin Amurka.
2015 Jan 22 , 23:37
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran a lokacin da yake ganawa da dubban mutanen birnin Qom ya bayyana cewa, kawo rarraba tsakanin al’umma da kowane suna ya yi hannun riga da abin da al’ummar take bukata.
2015 Jan 08 , 10:12
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gana da wasu daga cikin kwamandoji da jami'an dakarun sojin ruwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a jawabin da ya gabatar yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ruhin gwagwarmaya da tsayin daka a matsayin abin da ke kare mutumci.
2014 Dec 29 , 19:03
Bangaren kasa da kasa, a safiyar yau ne shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bude taron kasa da kasa don fada da tsaurin ra’ayi da tashin hankali na kwanaki biyu a nan birnin Tehran don tattaunawa kan barazanar da duniya take fuskanta daga wadannan abubuwa biyu.
2014 Dec 09 , 21:49