IQNA

Mutanen Kasar Zimbabwe Ba Su Da Masaniya Kan Mazhabar Ahlul Bait

23:54 - May 21, 2015
Lambar Labari: 3306226
Bangaren kasa da kasa, bisa la’akari da akasarin musulmin kasar Zimbabwe yan sunna ne ba su da cikakkiyar masaniya kan mazhabar shi’a wato tafarkin iyalan gidan manzo


William Hashem Shweila makarancin kur’ani dan kasar Zimbabwe a zanatarwasa da kamfanin dilalncin labaran kur’ani mai tsarki na Iqna ya bayyana cewa, kasarsa na da mutane kimanin miliyan 14, kuma kasha biyu cikin dari ne kawai mabiya addnin muslunci.

William Hashem y ace wannan dai bas hi ne karon farko da yake halartar gasar karatu da haradar kur’ani mai tsarki ba, domin kuwa  acikin shekara ta 1997 ya halarci gasar Masar, haka nan kuma  acikin shekara ta 1998 ya halarci gasar kur’ani a Saudiyyah.

Ya ci gaba da cewa kos hakka babu hakan ya bar babban tasiria  cikin zuciyarsa, kasantuwar yana rayuwa a cikin wata kasa wadda ba ta musulomi ba, kuma musulmi su ne mafi karanci a cikin marassa rinjaye, amma kuma duk da hakan ya samu damar hardace kur’ani mai tsarki tun yan ada n shekaru 17 da haihuwa.

Wanann na daga cikin abin da ya saya shi mayar da hankali domin jawo hankulan sauran musulmi da suke kasar domin su bayar da himma wajen isar da sakon kur’ani mai tsarki ga sauran mutanen kasarsa da bas u da masaniya kan addinin muslunci.

Dangane da batun yaduwar mazhabar iyalan gidan manzo kuwa, ya bayyana cewa yanzu haka dai da dama daga cikin musulmin kasar bas u da cikakkiyar masaniya kan wannan tafarki, domin kuwa babban abin da suka sani shi ne abin da ya je musu na daga koyarwar bangaren sunna.

Dangane da yanayin rayuwar muslmin kasar Zimbabwe kuwa, ya bayyana cewa suna rayuwa tare da sauran mutane lami lafiya, kuma ba su da wani tufafi da ya kebance su, suna saka kaya kamar na al’ummar kasar, sai dai wasu lokuta sukan saka kaya na musamman a lokutan na musamman da suka kebance su.

3305793

Abubuwan Da Ya Shafa: zimbabwe
captcha