IQNA

Kasashe 50 Za Su Halarci Taron Tattalin Arziki Tsakanin Rasha Da Duniyar Musulmi

23:15 - May 15, 2017
Lambar Labari: 3481518
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar Rasha ta sanar da cewa wakilai daga kasashe 50 ne na duniya za su halarci taron tattalin arziki tsakain Rasha da duniyar musulmi a Qazan.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan taro shi ne irinsa na farko da Rasha za ta dauki nauyin gudanar da shi, wanda zai samu halartar baki dubu 2 daga kasashen duniya, wanda ya hada da jami'an gwamnatoci, da wakilan kamfanoni da kuma masana kan harkokin tattalin arziki, gami da masu saka hannayen jari.

Shugaba Vladimir Putin ne da kansa ya baiwa shugaban Jamhuriyar Tataristan umarnin shirya gudanar da taron, da kuma jagorantar kungiyar bunkasa tattalin arziki tsakanin Rasha da msuulmi.

Daga cikin muhimamn abubuwan da zaman taron zai mayar da hankali a kansu akwai batun gudanar da harkokin kasuwanci na hadin gwiwa a tsakanin kamfanonin Rasha da kuma kamfanonin muslunci, daga ciki kuwa har da kamfanonin da ke samar da kayan abincin Halal tare da hadin gwiwa da kamafanin «Russia Halal Expo» kamar yadda za a tatatuna batun saka hannayen jari a tsakanin Rasha da kuam manyan 'yan kasuwa musulmi.

3599596


captcha