IQNA

Baje Kolin Littafai A birnin Harare Na Zimbabwe

23:45 - October 30, 2018
Lambar Labari: 3483085
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da gudnar da bajen kolin littafai na kasa da kasa a birnin Harare na Zimbabwe.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da gudnar da bajen kolin littafai na kasa da kasa a birnin Harare na Zimbabwe an raba kwafin kur’ani da aka tarjama a cikin harshen turanci.

Wannan kur’ani an tarjama shi ne a cikin harshen turanci a kasar Iran, wanda kuma bangaren littafan kasar ne da ke halartar wannan baje koli ya raba kwafin kur’ani ga dukkanin wadanda suka ziyarci wurin.

Shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, manufar raba wannan kwafin kur’ani ita ce, taimaka ma wadanda suke bukatar sanin wani abu dangane da kur’ani da suke fahimtar harshen turanci.

Duk da cewa musulmin kasar Zimbabwe su ne martassa rinjaye a kasar, amma suna zaune lafiya tare da mabiya addinin kirista wadanda su ne masu rinjaye a kasar.

3759841

 

 

 

 

captcha