IQNA

Mahukuntan Thailand Na Tsare Da Wasu Jagororin Ikhwan

22:34 - March 08, 2019
Lambar Labari: 3483437
Jami’an tsaron kasar Thailand sun kame wasu jangororin kungiyar Muslim Brotherhood su 4 a filin sauka da tashin jiragen sama na Bankuk.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Jami’an tsaron kasar Thailand sun kame wasu jangororin kungiyar Muslim Brotherhood su 4 a lokacin da suka iso filin sauka da tashin jiragen sama na Bankuk fadar mulkin kasar a jiya daga kasar Malayzia.

Kungiyar Ikhwan na ci gaba da tuntubar mahukuntan kasar Thailand da suka hada da Firayin ministan kasar gami da ministan harkokin waje, domin yin kira gare su da kada su mika wadannan mutane ga gwamnatin kasar Masar.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin Masar tana neman wadannan mutane domin kame su, inda suke zaune a kasar Malayzia bayan da suka tsere daga kasar ta Masar domin gudun cutarwa daga mahukuntan kasar.

Gwamnatin Malayzia dai ta fitar da wadannan mutane 4 daga cikin kasarta, inda suka nufi Thailand, a can kuma ana tsare da su a filin sauka da tashin jirgin sama na Bankuk da nufin mika su ga gwamnatin Masar.

3796144

 

captcha