IQNA

Hamas Ta Bukaci Saudiyya Da Ta Saki Falastinawa Da Take Tsare Da Su

22:56 - May 07, 2020
Lambar Labari: 3484772
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta bukaci masarautar Saudiyya da ta saki Falastinawa da take tsare da su ba tare da wani dalili ba.

A cikin wani bayani da ya saka a shafinsa na twitter, kakakin kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya bayyana cewa, ya kamata masarautar Saudiyya ta saki Falastinawa da take tsare da su ba tare da sun aikata wani laifi ba.

Ya ce duk wata kasa da take da’awar cewa tana goyon bayan al’ummar Falastinu dangane da zalunci da mamayar da suke fuskanta daga yahudawa, ya kamata ne ta taimaka musu, maimakon kame su da tsare su a cikin gidajen kurkuku ba tare da wani laifi ba.

Tun fiye da shekara guda da ta gabata ce gwamnatin Saudiyya ta kame Falastinawa masu yawa, ta kuma jefa su kuruku, bisa hujjar cewa su mambobin kungiyar Hamas ne, ko kuma suna goyon bayan kungiyar.

 

3897072

 

captcha