IQNA

Sabon Shirin Ajiyar Kudade A Najeriya Domin Tafiya Aikin Hajji

18:01 - February 22, 2021
Lambar Labari: 3485679
Tehran (IQNA) An fara aiwatar da wani sabon shiri da aka bullo da shi a Najeriya na ajiyar kudade domin tafiya aikin hajji.

Shafin Nairamitrics ya bayar da rahoton cewa, a halin yanzu an fara aiwatar da shirin karbar kudin ajiya a bankin Jaiz da ke Najeriya, domin taimaka masu bukatar zuwa aikin hajji wajen tara kudadensu.

Wannan shiri an fara aiwatar da shi ne biyo bayan wani hadin gwiwa da aka yi tsakanin hukumar alhazai ta kasa da kuma bankin na Jaiz, inda a halin yanzu shirin ya fara aiki a  hukumance.

Mukaddashin babban darakta na bankin Jaiz a Najeriya Isma’il Adamu ya bayyana wannan shiri da cewa, yana daya daga cikin muhimman ayyuka da bankin ya kirkiro a najeriya, wadanda za su taimaka ma musulmi masu son tafiya aikin aikin hajji, musamman marasa karfi daga cikinsu.

Ya ce yanayin tsarin ajiyar kuadden yana a matakai daban-daban ne, akwai mataki na gajeren zango, akwai mataki na matsakaicin zango, akwai kuma mataki na dogon zango, wanda mutum yana da zaben daukar kowane mataki yake bukata daidai karfinsa.

Baya ga haka kuma ya yi ishara da cewa, wadanda suka ajiye wadannan kudade za su amfana da abin da za su samu daga mu’amalar da za a yi da kudaden, domin kuwa ana raba amfanin da aka samu ne daidai da abin da yake rubuce a cikin ka’idojin bankin, wanda suka ginu a kan mahangar cinikayya da hada-hadar kudade bisa mahangar addinin muslunci.

3955612

 

captcha