IQNA

Gwamatin Isra'ila Tana Ci Gaba Gina Matsugunnan Yahudawa A Yankunan Falastinawa

18:56 - October 30, 2021
Lambar Labari: 3486491
Tehran (IQNA) gwamnatin yahudawan Isra'ila ta yi biris da dukkanin kiraye-kirayen da ake yi mata na ta dakatar da gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wani jami'i na kusa da Firaministan Isra'ila Naftali Bennett ya bayyana cewa "Gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ba za ta hana gina matsugunan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan ba.

Haka nan kuma a cewar Gwamnatin Bennett tana sa ran gwamnatin Biden na da niyyar sake bude karamin ofishin jakadancinta a birnin Kudus.

A ranar 27 ga Oktoba, kwamitin tsare-tsare na Ma'aikatar Yakin Isra'ila ta amince da gina gidaje 3,144 da ba bisa ka'ida ba a Yammacin Gabar Kogin Jordan.

Wannan karon farko tun bayan shugabancin Joe Biden, Isra’ila ta kudiri aniyar gina matsugunnan yahuadawa a cikin yankunan Falastinawa da ek gabar yamma da kogin Jordan.

Yanzu haka dai akwai matsugunan yahudawa 13 da Isra’ila ta gina ba bisa ka'ida ba a Gabashin Kudus, da kuma wasu 253 a Yammacin Kogin Jordan, inda Yahudawa sama da 660,000 suke.

A karkashin dokokin kasa da kasa, ana daukar dukkan matsugunan Yahudawa da aka gina a cikin yankunan Falasdinawa da cewa aiki ne na mamaya wanda ba ya bisa ka’ida.

Wani jami'in Isra'ila ya ce ana ci gaba da gina matsugunan yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye ba tare da wani cikas daga gwamnatin Biden ba.

 

4009116

 

 

captcha