IQNA

Fatan samun bunkasuwar tattalin arzikin musulmi a shekarar 2022

22:37 - February 03, 2022
Lambar Labari: 3486902
Tehran (IQNA) Ana da fatan samun ci gaban harkokin tattalin arziki na musulmi a cikin wannan shekara da muke ciki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, bisa hasashen masana, kamar yadda rahotannin hukumomin ƙididdiga suka nuna, ƙaruwar farashin mai a duniya a shekarar 2021 da yawaitar allurar rigakafin corona da rage cututtukan zuciya zai sa tsarin hada-hadar kuɗi na Musulunci tare da tattalin arzikin duniya ya sami bunƙasa sannu a hankali tare da komawa daidai.

Tattalin arzikin Musulunci a shekarar 2021 ya samu ci gaba da binkasa, duk da ci gaba da yaduwar corona da shakkun yiwuwar kawo karshenta, 

Wannan ya sanya rahotannin kudi na 2022  suka kasance masu karfafa gwiwa, kuma suna nuna ci gaban wannan fannin a kasashe da yawa.

Hasali ma dai ana iya cewa fannin ba da tallafin kudi na Musulunci, bayan tsayin daka da ya yi a shekarar 2020, ya bar kyakkyawan sakamako a shekarar 2021, saboda ingantaccen tsarin tattalin arziki, da kara yawan manyan ayyuka da kuma mai da hankali kan abubuwan da suka shafi muhalli, zamantakewa. 

A cewar hukumar kididdiga ta duniya S&P, duk da kalubale biyu na Covid-19 da raguwar farashin mai a duniya, kadarorin wannan fanni sun karu da kashi 10.6% a bara.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4031288

captcha