IQNA

Babban Muftin Oman Ya Yi Allawadai Da Hana Saka Hijabi A India

23:29 - February 13, 2022
Lambar Labari: 3486945
Tehran (IQNA) Mufti na Oman ya yi kira ga mahukuntan Indiya da su mutunta hakkin musulmin kasar.

Babban malami Mufti na Oman ya yi kira ga mahukuntan Indiya da su mutunta hakkin musulmin Indiya, kamar yadda a lokacin mulkin musulmi a kasar wadanda ba musulmi ba, ba su ganin komai sai mutuntawa da adalci daga masu mulki a kasar.

Shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Khaleej Online cewa, Sheikh Ahmad bin Hamad Al-Khalili, Mufti na kasar Oman, ya yi Allah wadai da matsin lamba da muzgunawa musulmin Indiya, musamman mata, tare da yin kira da a samar da mafita a kasar.

Al-Khalili ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Musulman Indiya a shafinsa na Twitter, yana mai cewa gwamnatin Modi mai tsatsauran ra'ayi a Indiya tana yin abin  Allah wadai, musamman cin zarafin dalibai musulmi da aka yi a baya-bayan nan da kuma hana su shiga jami'a saboda sanya hijabi.

Mufti na Oman ya ce: "Labari mai ban tausayi har yanzu yana zuwa mana daga Indiya, masu tsattsauran ra'ayi na can suna samun sabbin abubuwa a kowace rana don muzgunawa da kai wa musulmi hari."

Ya kara da cewa: "A karshe dai an matsa wa mace musulma 'yar kasar Indiya lamba a cikin hijabi na addini, kuma wannan lamari ne da ya shafi cin zarfin addini."

Sheikh Al-Khalil ya ce: "An san cewa kasar Indiya ta shafe shekaru aru-aru da shuwagabannin musulmi suke mulkin kasar, kuma babu wani abu da ake yi face girmama shugabannin sauran addinai a cikin akidarsu da ibadarsu da dukkan al'adunsu."

 

 

4036045

 

 

 

 

captcha