IQNA

Halin da ake ciki a hubbaren Imam Ali (AS) a ranar Idin Ghadir

15:00 - July 18, 2022
Lambar Labari: 3487561
Tehran (IQNA) a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Idin Ghadir Haramin Imam Ali (AS) na karbar masu ziyara daga larduna daban-daban na kasar Iraki da wasu kasashen Larabawa da na Musulmi.

Hubbaren Imam Ali (AS) da ke Najaf Ashraf cike yake da masu ziyara da suka zo wannan wuri mai alfarma daga larduna daban-daban na kasar Iraki da wasu kasashen Larabawa da na Musulunci a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Idin Ghadir.

Kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iqnaya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Iraki cewa, hubbaren Alawi mai alfarma da ke birnin Najaf Ashraf a yau, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan sallar Idi Ghadir Kham, ya karbi bakuncin masu ziyara da suka zo wannan wuri mai alfarma daga yankuna daban-daban na kasar Iraki da wasu kasashen duniya domin gudanar da wannan gagarumin idi na musulmi.

Alokaci guda kuma an kawata sassa daban-daban na hubbaren Alawi mai alfarma, an kawata su da furanni da haske, da kuma sanya alluna da ke nuni da jaddada mubaya'a ga Imam Ali (a.s.).

https://iqna.ir/fa/news/4071702

captcha