IQNA

Hamas: Daidaita alaka da Isra’ila na hadari ga musulmi da Larabawa

15:52 - July 25, 2022
Lambar Labari: 3487591
tEHRAN (iqna) kungiyar gwagwarmaya  ta Hamas ta bayyana duk wani mataki na daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawa  a matsayin hadari ga al'ummar Larabawa da Musulmi

A yayin da take jinjina kan ‘yan gwagwarmayar Falastinawa na Nablus kan turjiya da suke yi wajen fuskantar yahudawa  ‘yan mamaya, kungiyar gwagwarmaya  ta Hamas ta bayyana duk wani mataki na daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawa  a matsayin hadari ga al'ummar Larabawa da Musulmi, tare da yin kira ga kasashen Larabawa da na Musulmi das u guji kulla duk wata alaka makamanciyar haka da Isra’ila.

A rahoton kafar yada labar5ai ta Saut al-Quds ta bayar, Ismail Ridwan daya daga cikin jagororin kungiyar Hamas a wata hira da ya yi da wannan tasha,  ya bayyana daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan a matsayin hadari babba  ga al'ummar musulmi baki daya.

A cewarsa, manufar wasu gwamnatocin kasashen Larabawa ita ce daidaita alaka da gwamnatin sahyoniyawan, da kulla alkoki siyasa, zamantakewa da tattalin arziki, domin kawar da hankula daga batun Falastinu.

 Rdwan  ya jaddada cewa, kulla alaka tsakanin kasashen larabawa da Isra’ila, yana a matsayin halasta wa Isra’ila zaluncin da take yi kan al’ummar falastinu ne, da kuma keta alfarmar wuraren addinin muslunci da suke Falastinu da suka hada da masallacin Quds mai alfarma.

 

4073258

 

captcha