Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alkahira 24 cewa, Fatemeh Al-Bandari wata ‘yar kasar Masar da ta halarci gasar kalubalen karatu a matakin kasar Masar a matsayin wakiliyar Azhar kuma ta yi nasara a matsayi na daya, ta sanar da hakan a wata hira da ta yi da gidan talabijin cewa: ina da shekaru 3 na fara da haddar Al-Qur'ani, kuma ina da shekara 4 na yi nasarar haddace gaba dayansa, sannan ina da shekara 13 na gama haddar Alkur'ani mai girma da ruwayoyi goma.
Ita dai wannan yarinya ‘yar kasar Masar, wadda a yanzu haka tana karatu a makarantun Sakandare na Al-Azhar ta kara da cewa: “Na yi nasara a matsayi na daya a gasar karatu da haddar litattafai na kasa a matakin lardi, kuma ya zuwa yanzu na samu nasarar haddar wasu abubuwa. hadisai na annabia sama da 6000 da baitoci sama da 1,000 na wakar larabci.
A baya dai ta taba lashe matsayi na daya a gasar karatun littafai na kasashen Larabawa da aka gudanar a birnin Dubai, kuma a lokacin ta samu karramawa da jinjina daga wakilin cibiyar Azhar.